Search
Close this search box.

Yemen: Sayyid Huthi Ya Ce Amurka Tana Yaudarar Mutane A Yakin Da Ke Faruwa A Gaza

Shugaban kungiyar Ansarullah na kasar Yemen sayyid Abdullamalik Badruddeen Huthi ya bayyana cewa shugaban kasar Amurka Joe Biden yana son yaudarar mutanen ne kawai, a

Shugaban kungiyar Ansarullah na kasar Yemen sayyid Abdullamalik Badruddeen Huthi ya bayyana cewa shugaban kasar Amurka Joe Biden yana son yaudarar mutanen ne kawai, a lokacinda ya fito ya bayyana cewa kasar Amurka zata dakatar da bawa HKI makamai ko kuma bad a yardarta ba sojojin HKI suka fara yaki a Rafah.

Majiyar kamfanin dillancin labarai ta IRIB-NEWS ta nakalto shugaban Ansarallah yana fadar haka a yau Alahamis ya kuma kara da cewa, babu abinda HKI zata yi ba tare da amaincewar gwamnatin Amurka ba, kuma da yardarta ne ta fara kai hare haren kan miliyoyin falasdinawa a garin Rafaha.

Sannan dangane da dakatar da bata makamai ma ba gaskiya bane, don wa zai san sanda zata aika da makaman.

Sayyid Huthi ya kammala da cewa Amurka bata son a dakatar da yaki a gaza, don haka kada kowa ya yaudaru da maganganun shugaba biden. Sannan hare haren da sosjojin HKI suke kaiwa Rafah ba falasdinawa kawai take kaiwa hare hare ba, sai dai hare haren sun hada hard a kasar Masar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments