Shugaban kasar Aljeriya ya bayyana cewa: An rusa duk wasu ayyukan bada agajin bil’Adama a Falasdinu
Shugaban kasar Aljeriya Abdul-Hamid Taboune ya bukaci dukkanin kungiyoyin kasa da kasa da cibiyoyin bada agajin bil’Adama da su yi aiki da hakkin da ya rataya a wuyarsu wajen ganin an kawo karshen kisan kiyashin da ake yi wa Falasdinawa musamman al’ummar Zirin Gaza.
Taboune ya jaddada cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana aiwatar da kisan kiyashi kan Falasdinawa da suke Gaza, don haka dole ne a kan cibiyoyin kasa da kasa su tabbatar an yi aiki da kundin kare hakkin bil’Adama wajen kare Falasdinawa.