Dakarun kungiyar Hamas da kuma sauran kungiyoyin falasdinawa a gaza, sun shiga fafatawa mai tsanani da sojojin HKI a garin Zaitun da kuma garin Rafah na zirin gada, inda suke kokarin hana kutsawar tankunan yaki na yahudawan a wadannan yankuna.
Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa mayaka Falasdinawa sun shiga fafatawa da sojojin yahudawan a kudu maso yammacin garin zaitun da ke kudu maso gabacin zirin gaza.
Dan rahoton almayadeen ya kara da cewa tankunan yakin sojojin HKI sun fara kutsawa cikin unguwannan zaitun da Tel hawa har ma sun bulla a kan tito na 8, inda masallacin Ali yake a garin na zaitun.
Dakarun Kassam sun ce sun yi amfani da makamin ‘Tondoom’ don hana wani tankin yanki yahudawan kara shiga cikin unguwar. Hakama dakarun saraya qudus sun bayyana cewa sun yi luguden wuta kan cibiyar sojojin yahudawa a yankin tare da amfani da makamin “Hawun”.