Search
Close this search box.

Yemen: Mayakan Ansarullah Sun Kai Hari Kan Jiragen Ruwan Isra’ila A Tekun Aden

Kungiyar Ansar Allah (Houthis) ta sanar a ranar Alhamis din nan cewa ta kai hari kan jiragen ruwan Isra’ila “MSC DEGO” da “MSC GINA” a

Kungiyar Ansar Allah (Houthis) ta sanar a ranar Alhamis din nan cewa ta kai hari kan jiragen ruwan Isra’ila “MSC DEGO” da “MSC GINA” a mashigin tekun Aden.

A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce: An kai harin ne da makamai masu linzami da jirage marasa matuka, kuma harin ya yi nasara.

Sanarwar ta kara da cewa: “Rundunar sojin ta Yemen ta ce ta yi amfani da makami mai linzami wajen kai harin a kan jirgin ruwan MSC VITTORIA, na farko a cikin tekun Indiya, dayan kuma a kan wani jirgin ruwan tekun Arabiya, kuma harin ya shi ma ya yi nasara.

Ya yi nuni da cewa: Sojojin kasar Yemen suna bin abubuwan da suke faruwa a yankin zirin Gaza, kuma ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen zafafa kai hare-haren soji don daukar fansa kan zaluncin da  al’ummar Palastinu ke fuskanta daga Isra’ila, kamar yadda suka bayyana a cikin bayanansu na baya.

Houthis sun jaddada cewa: Dakarun kasar Yemen za su ci gaba da hana zirga-zirgar jiragen ruwa na haramtacciyar kasar Isra’ila zuwa tashar jiragen ruwa na Palastinu da Isra’ila ta har sai ta kawo karshen harin da kuma wuce gona da iri kan al’ummar Palasdinu a zirin Gaza. tsaya.”

Amurka da Birtaniya dai na zargin ‘yan Houthis da yin barazana ga ‘yancin zirga-zirgar jiragen ruwa a tekun Red Sea da Gulf of Aden, yayin da kungiyar Ansar Allah ta bayyana cewa jiragen ruwan da suke da alaka da Isra’ila ne kawai suke kai hari a yanayin da suke taimakawa wa Isra’ila wajen al’ummar zirin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments