Search
Close this search box.

Shugaban Kasar Iran Yayi Kira Ga Kasashen Duniya Su Taimakawa Mutanen Gaza

Shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya yi kira ga kasashen duniya su taimakawa mutanen gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye. Kamfanin dillancin labaran

Shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya yi kira ga kasashen duniya su taimakawa mutanen gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto shugaban yana Fadar haka a taron ranar  kungiyar agaji ta ‘hillar Ahmar’ ko red cross’ ta duniya a nan Tehran. Ya kuma kara da cewa yana kirin duk wanda yake da zuciya mai tausayi ko kuma yake da dan’adamtaka  a cikin zuciyarsa ya kawo dauki wa al-ummar falasdinu, musamman na gaza wadanda sojojin HKI suka yiwa kawanya ta sama kasa da kuma ruwa.

Shugaban ya kara da cewa yana taya dukkan yayan kungiyar ta Red Crescent ta bada agaji a duniya murnar zagayowar ranarsu, da kuma yi masu jaje kan abokan aikinsu wadanda sojojin HKI suka  kashe a gaza a lokacinda suke gudanar da ayyukansu na bada agaji.

Tun ranar 7 ga watan Octoban shekarar da ta gabata ce, sojojin HKI suka farwa mutanen gaza da yaki da nufin share kungiyar Hamas daga doron kasa da kuma kwato yahudawan da take tsare da su a gaza. Kuma ya zuwa yanzu sojojin sun kashe Falasdinawa fiye dubu 35 a yayinda wasu fiye da dubu 78 sun ji rauni.

Ranar 8 ga watan mayu na ko wace shekara ne ranar kungiyar bada agaji ta red cross a  duniya. Ko Red Crescent a kasashen musulmi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments