Search
Close this search box.

Iran Ta Ce Tana Iya Sauya Ra’ayinta Dangane Da Mallakar Makaman Nukliya Idan Ta Ga Wata Barazanar Da Zata Shafe Kasar

Shugaban kwamiti  ayyuka na musamman a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya jaddada matsayin JMI na haramcin mallakan makaman nukliya, amma duk haka  idan akwai

Shugaban kwamiti  ayyuka na musamman a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya jaddada matsayin JMI na haramcin mallakan makaman nukliya, amma duk haka  idan akwai barazana wacce zama hana wanzuwar kasar, tana iya sauya ra’ayinta dangane da mallakar makaman na nukliya.

Kamafanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto Kamal Kharazi shugaban kwamiti ayyuka na na musamman a ma’aikatar harkokin wajen kasar yana fadar haka, a hirar da ta hada shi da tashar talabijin ta Aljazeera ta kasar Qatar.

Kharrazi ya kara da cewa idan HKI ta kuskura ta kaiwa cibiyoyin nukliyar kasar Iran hare hare, maida martanin da Iran za ta yi zai kasance na musamman ne. Har’ila yau Iran tana iya sauya ra’ayinta dangane da mallakar makaman Nukliya, sabanin wanda ta ke kansa a baya.

Kharrazi ya kara da cewa, warware matsalar Falasdinu ta hanya kafa kasashe biyu a wajen Iran ba mai yuwa bane. Amma Iran tana fatan a kafa kasar Falasdinu wacce dukkan mabiya addinai daban wadanda suka hada da, Musulmi, kiristoci da yahudawa zasu rayu karkashin ta.

Daga karshe yace Iran zata ci gaba da goyon bayan kawancen masu gwagwarmaya a yankin don kwato hakkinsu  daga wadanda suka zaluncesu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments