‘Yan sandan Amurka suna ci gaba da murkushe daliban jami’a da suke gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga al’ummar Falasdinu
Tashar talabijin ta NBC News ta Amurka ta watsa rahoton cewa: Rundunar ‘yan sandan Amurka sun farma daliban jami’ar Geoge Washinton da suka fito zanga-zangar nuna goyon baya ga al’ummar Falasdinu, inda ‘yan sandan na Amurka suka kwashe tantunan da daliban suka kafa domin gudanar da zaman dirshen.
Kamar yadda ‘yan sandan na Amurka suka harba iskar gas mai sanya hawaye kan daliban tare da kame wasu daga cikinsu da suka haura hamsin, daliban jami’ar dai sun fito ne suna rera taken ‘Yanci ga Falasdinawa da jaddada yin kiran nesantar kai harin wuce gona da iri kan birnin Rafah.