HKI Ta Bada Umurnin Rufe Ofishin Tashar Talabijin Ta Al-Jazeera A Kasar

Majalisar ministocin HKI ta bada umurnin a rufe ofishin tashar talabijin ta Aljazeera da ke birnin Nasirah a cikin kasar Falasdinu da aka mamaye. Kamfanin

Majalisar ministocin HKI ta bada umurnin a rufe ofishin tashar talabijin ta Aljazeera da ke birnin Nasirah a cikin kasar Falasdinu da aka mamaye.

Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya bayyana cewa ministan sadawar na haramtacciyar kasar ne ya bada wannan sanarwan.  Ya kuma kara da cewa za’a rusa dakin shirye shiye na tashar dake garin nasirah sannan a kwace dukkankayakin aiki na watsa labarai da tashar take da su a cikin kasar.

Sholumu Kar’ii ministan watsa labaran HKI ya kara da cewa, tare da haka gwamnatin haramtacciyar kasar zata dakatar da watsa shirye shiryen Aljazeera daga kasar Falasdinu da aka mamaye a cikin harsunan Larabaci da kuma turanci.

Tashar talabijin ta Aljazeerah dai mallakin kasar Qatar ce kuma ta fara aiki a kasar Falasdinu da aka mamaye ne fiye da shekaru 10 da suka gabata, a cikin harsunan larabci da kuma turanci.

Banda haka sojojin haramtacciyar kasar sun kashe ma’aikatan tashar da dama kafin haka.

Daga cikin wadanda ta kasha dai akwai shirin Abu akila da kuma Samir Abu –diqqa, Hamza Addahdud wadanda suka yi shahada a gaza a lokacinda sojojin hki suka cilla makamai kan ofishin tashar da ke gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments