rahotanni daga Nigeria sun nuna cewa masu sha’awar kwallon kafa a kasar sun bukaci shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta korar shugabannin hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar ta NFF, domin maye gurbin su da wadanda suka kira da kwararru da za su ceto kwallon Najeriya daga tabarbarewa.
Wannan kira ya biyo bayan tarin rashin nasarar da kungiyoyin kwallon kafar kasar suke fuskanta ne a wasannin da suke yi a nahiyar Afirka.
Daga cikin jerin rashin nasarar akwai gazawa wajen samun damar zuwa gasar cin kofin duniyar da aka kammala a Amurka da Canada da kuma Mexico, sai kuma ficewa daga gasar mata da Super Falcons tayi a jiya, a gasar dake gudana a Morocco, a daidai lokacin da Burkina Faso ke fitar da kungiyar matasa ƴan kasa da shekaru 20, wato Flying Eagles, wajen hana su damar zuwa gasar cin kofin Afirka da duniyar da za’ayi baɗi.
Wadannan rashin nasarori ana danganta su da rashin shugabanci na gari dake gudana a karkashin jagorancin shugaban hukumar NFF Ibrahim Gusau, wanda a halin yanzu ke shugabancin jagorancin hukumar.
Fitaccen marubucin ya ce abinda ake bukata shi ne gudanar da taro na masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa domin lalubo hanyoyin da suka dace na farfado da kwallon kafar Najeriya da kuma dawo da kimar ta, maimakon bai wa wadannan shugabanni damar zarcewa.