Ziyarar Arba’in: Mutane Miliyan 2 Su Ka Shiga Iraki Daga Iran

Jami'in 'yan sandan Hussaini ya kuma masu fita daga Iran din karuwa yake yi. A kowace shekara miliyoyin masoya iyalan manzon Allah ( s.a.w) ne
Masu Zuwa Iraqi Ziyara

Babban jami’in ‘yan sanda na rundunar “Faraja” ya bayyana yadda mutanen Iran suke kwarara zuwa kasar Iraki domin halartar ziyarar arba’in ta shahadar Imam Hussain ( a.s).

Jami’in ‘yan sandan ya ce, kamar yadda aka saba a shekarun da su ka  gabata,jami’an tsaro suna ci gaba da kuma da yadda masu Ziyara suke fita daga Iran ta mashigar iyakoki 5 na gundumomin Iran, da su ka hada Ilam, Kerman sha, Khuzestan, Kurdistan da kuma Azeraijab ta yamma.

Haka nan kuma sanarwar ta ‘yan sanda ta ce, kusan 98% na masu Ziyara suna ratsawa ne ta cikin iyakar ta hanyar amfani da motocinsu da kuma na haya.

Haka nan kuma ya kara da cewa;A cikin kwanaki 13 da su ka gabata kawai,adadin mutanen da su ka ketare iyaka daga Iran zuwa Iraki sun kai miliyan 2.

Jami’in ‘yan sandan Hussaini ya kuma masu fita daga Iran din karuwa yake yi. A kowace shekara miliyoyin masoya iyalan manzon Allah ( s.a.w) ne suke shiga cikin kasar Iraki domin juyayin 40 daga ranar shahadar Imam

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted