Iran ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan hare-haren da Amurka da Saudiyya suka kai wa Iraki
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi Allah wadai da harin da Amurka da Saudiyya suka kai wa wasu yankuna a Iraki.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi Allah wadai da harin da Amurka da Saudiyya suka kai wa wasu yankuna a Iraki, ciki har da hare-haren da suka kai kan cibiyoyi da hukumomin kasar da kuma jerin gwano da masaukin masu zayarar juyayin Arba’in Imam Hussain (a.s) jikan Manzon Allah {s.a.w}.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Wadannan hare-haren sun zama wani hari a fili kan ikon mallakar kasa da kuma cikakken yankin Iraki, wanda hakan ya saba wa Mataki na 2, Sashi na 4 na Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya da kuma muhimman ka’idojin dokokin kasa da kasa, kuma wani bangare ne na burin Amurka da Sahayoniyya na fadada yaduwar yaki da rikici a yankin Yammacin Asiya.
Yayin da take bayyana ta’aziyyarta kan shahadar wasu ‘yan asalin Iraki masu daraja sakamakon wadannan hare-haren, Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta tabbatar da cikakken goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga gwamnatin Iraki da al’ummarta. Tana dora alhaki kan gwamnatin Amurka da kawayenta da ke yankin da hannu a cikin mummunan sakamakon wadannan ayyukan ta’addanci, rashin tausayi, da kuma tayar da hankali.