Jami’an Tsaron Iran Sun Rusa Wasu Gungun ‘Yan Ta’adda A Kudu Maso Gabashin Kasar

Jami’an tsaron Iran sun wargaza wasu gungun ‘yan ta’adda guda hudun masu kafirta musulmi a yankin kudu maso gabashin Iran Ma’aikatar Leken Asiri ta Iran

Jami’an tsaron Iran sun wargaza wasu gungun ‘yan ta’adda guda hudun masu kafirta musulmi a yankin kudu maso gabashin Iran

Ma’aikatar Leken Asiri ta Iran ta sanar da cewa ta wargaza wasu gungun ‘yan ta’adda guda hudu masu kafirta musulmi da kuma kame wasu ‘yan ta’adda 15 a yankin kudu maso gabashin kasar.

Sanarwar Ma’aikatar Leken Asiri ta Iran ta bayyana cewa: A cikin tsarin ayyukan kai hari da kariya da rundunar Babban Darakta na Ma’aikatar Leken Asiri ta kasar ke gudanarwa a Sistan da Baluchestan, an gano wasu gungun ‘yan ta’adda guda hudu wadanda suke karkashin kungiyoyin ta’addanci masu kafirta musulmi masu alaka da hukumomin leken asiri na makiya Amurka da ‘yan Sshayoniyya, nan take bayan shiga kasar, kafin su samu damar duk wani aikin barna.

A cikin jerin ayyukan da jami’an leken Asiri na Ma’aikatar Leken Asiri suka gudanar a lardin, a biranen Zahedan, Chabahar, Iranshahr, Khash, Taftan, Nikshahr, da Qasr-e Qand, an kama manyan mutane goma sha biyar na kungiyoyin da ke jagorancin gungun ‘yan ta’addana, kuma an kwace wasu bindigogin da harsasai daga hannunsu.

Waɗannan ‘yan ta’adda da suke da alaƙa da Amurkawa da ‘yan Sahayoniyya, sun yi niyyar aiwatar da ayyukan maƙiyi na wargaza tsaron lardin da kuma kai hari ga cibiyoyin tattalin arziki, ma’aikatar shari’a, da sauran kayayyakin more rayuwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted