Rahotanni da kamfanin Tasnim na kasar iran ya nakalto ya nuna cewa a yau juma’a kungiyar hizbullah ta fitar da wani bayani, inda tayi tir da harin da kasar Amurka ta kai kasar Iraqi kuma ta bayyana shi a a matsayin keta hurumin kasar kuma babban hadari ne ga alummar kasar Iraqi, kuma ya keta dokokin kasa da kasa .
kungiyar hizbullah ta fitar da wannan bayani ne bayan harin hadin guiwa da Amurka da kasar Saudiya suka kai a sansanin kungiyar Hashdu shaabi na kasar Iraqi, kuma yayi sanadiyar shahadar mutane 20 tare da jikkata wasu guda 32 da zargin cewa ta kai mata hari a cibiyar manfetur dinta , lamarin da ta karyata kuma ta bayyana shi a matsayin fakewa ne don rufe gazawarta kan kasar Yamen
hizbullah ta ce wannan harin zai taimawa kasar Amurka da isra’ila ne kawai da nufin wargaza zaman lafiya da tsaron yanki, ta jaddada cewa zubar da jinin alummar Iraqi da kasar Amurka take yi ya tona asirin bakar aniyarta ta fadada hare harenta domin hana kasar iraki zaman lafiya.
daga karshe ta bayyana cewa ya kamata kasar saudiya ta koma tattaunawa da bude kofar diflomasiya tare da gwamnatin iraki domin warware duk wata matsala, mai makon a hada kai da ita wajen kai mata hari