Rahotanni sun nuna cewa An cimma yarjejeniyar kwancewa kungiyar Hamas Dammara a Zirin Gaza, wanda shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana a matsayin babban ci gaba ga shirin samar da zaman lafiya na Board of Peace.
Wannan mataki ya biyo bayan watanni da aka kwashe ana tattaunawa tsakanin Hamas da kasashen da suka shiga tsakani kamar su Masar, Qatar, da Turkiyya. Yarjejeniyar ta tanadi cewa Hamas za ta mika makamanta a cikin matakai daban-daban, sannan sojojin Isra’ila za su fice daga yankin Gaza.
A karkashin wannan yarjejeniya, Hamas za ta mika dukkan makamanta ga wata hukuma ta musamman mai suna National Committee for the Administration of Gaza (NCAG), inda kungiyar ta jaddada cewa ba za ta mika makamanta kai tsaye ga rundunar Isra’ila ba.
Babban sharaɗin da Hamas ta gabatar shi ne, dole dukkan matakan kwance damarar su tafi daidai da janyewar sojojin Isra’ila daga yankunan da suka mamaye. Su ma kasashen da suka shiga tsakani za su sanya ido domin ganin kowanne bangare ya cika alkawuransa.
Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa za a kafa wata sabuwar rundunar tsaro ta kasa da kasa wacce za ta yi aiki tare da jami’an ‘yan sandan Falasɗinawa don tabbatar da tsaro a yankin.