Rahotanni sun bayyana cewa miliyoyin mutane ne suka fito kwansu da kwarkwatansu a babban birnin San’a na kasar Yamen domin gudanar da zanga-zangar nuna adawa da kasar saudiya da hare-haren da ta kai kan kasar yamen, inda suka ta rera taken cewa idan aka killace su, to su ma za su killace saudiya a teku, idan kuma aka kai musu hari su ma za su mayar da martani.
Haka zalika sun nuna goyon bayan su ga shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar sayyid Abdulamalik Alhuthi na daukar duk matakin da ya dace wajen ganin an janye kawanyar zaluncin da kasar saudiya ta kakabawa kasar da kuma dukiyarta da ikonta .
A cikin bayanin da suka fitar sun bukaci a sanya takunkumin teku kan kasar saudiya domin mayar da martani kwatankwacin abin da saudiya ta yi, har sai an dage takunkumi, kana sun bukaci a mayar da martani mai tsanani kan hare-haren da kasar saudiya ke kai musu da jirage marasa matuki
Da yake bayani game da tunawa da zagayowar shahadar shugaban kungiyar Hamas Isam’il Haniya ya jaddada matsayinsu na ci gaba da nuna goyon bayan alummar falasdinu da kuma masallacin Kudus, da kuma tsayawa tare da alummar gaza, da kuma dukkan yan gwagwarmaya ,