A ci gaba da mayar da martani da dakarun kasar iran ke yi kan harin da kasar Amurka ta kai a tsibirin Qasham , dakarun sun sanar da kai hari kan sansanin Amurka dake Ahmad Jabir a kasar Kuwait, kuma sun jaddada cewa hari ko barazana zai kara wa kasar iran karfin hadin kai da kuma riko da kare kasarsu ne kawai.
Ofishin kula da hulda da jama’a na dakarun kare juyin musulunci na iran ya sanar a wani bayani da ya fitar a wani bangare na mataki 27 na farmakin tsayawa na martanin da aka mayar ga hare-haren da sojojin Amurka yan taadda suka kai a kasar, wannan yasa sojojin sama na kasar sun kai hari kan wuraren ajiya jiragen yaki da tsarin sadarwa na tauraron dan adam, da kuma rumbunan kayan yaki na rundunar sojin Amurka a sansanin Ahamd jabir dake kasar Kuwait.
A jiya Alhamis ma dakarun kare juyin musulunci na kasar iran sun kai hari kan sansanin sojin Amurka na Ali Salim dake kasar Kuwait wanda yayi sanadiyar lalata wasu jiragen sama marasa matuki guda biyu, da kuma rumbunan makamashin da ake amfani da shi a jiragen sama na sojan Amurka dake sansanin .
Iran ta kai hari a sansanonin sojin Amurka da wurare masu muhimmanci a yankin, haka kuma ta mayar da martani ga jiragen ruwa dake yukurin ketare mashigar Hurmuz ba bisa ka’ida ba, wanda har yanzu yake rufe saboda harin da Amurka take kai wa.