Mataimakin Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Muhimmancin Alakar Iran Da Afirka

Mataimakin Shugaban kasar Iran na farko ya bayyana cewa: Babu wata hujja da ke nuna gazawa a ci gaban dangantaka da Afirka Mataimakin Shugaban Kasa

Mataimakin Shugaban kasar Iran na farko ya bayyana cewa: Babu wata hujja da ke nuna gazawa a ci gaban dangantaka da Afirka

Mataimakin Shugaban Kasa na Farko na Iran, Muhammad Reza Aref, ya jaddada bukatar samar da cikakkiyar daburar bunkasa dangantakar Iran da nahiyar Afirka.

Aref ya jaddada muhimmancin samar da cikakkiyar dabarar fadada dangantaka tsakanin Iran da Afirka, yana mai bayyana cewa karfafa hadin gwiwa da kasashen Afirka ya kamata ya zama babban fifiko a kasa kuma babu wani dalili na yin sakaci da wannan hanya, wadda ke biyan bukatun dukkan bangarorin da kuma muradun kasa.

A yayin wani taro a “Hedikwatar Afirka,” Aref ya bayyana cewa nahiyar Afirka tana da karfin tattalin arziki da kasuwanci mai yawa wanda zai iya taimakawa tattalin arzikin kasashe. tare da shawo kan illolin yaƙe-yaƙe biyu da aka dora wa Iran kwanan nan, da kuma kawar da cikas daga waje, wannaa zai samar da dama ta fadada hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu, musamman a fannin kimiyya, fasaha, da masana’antu.

A karshen taron, Mataimakin Shugaban Kasa na Farko ya yi kira ga Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran da ta farfado da diflomasiyya da kuma kawar da cikas na tattalin arziki da cinikayya da Afirka. Ya jagoranci shirya dabarun ci gaba kuma ya umurci kungiyoyin aiki na musamman da su gabatar da shawarwarinsu na aiki cikin wata daya don amincewa da aiwatarwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted