Rundunar Tsoron Juyin Juya Hali Ta Kai Hari Kan Sansanin Sojin Amurka A Jordan

Rundunar tsaron juyin juya hali ta kai hari kan sansanin sojin sama da kuma hedikwatar rundunar sojin Amurka da ke Jordan Rundunar Sojojin Sama ta

Rundunar tsaron juyin juya hali ta kai hari kan sansanin sojin sama da kuma hedikwatar rundunar sojin Amurka da ke Jordan

Rundunar Sojojin Sama ta Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ta sanar da cewa ta kai hari kan sansanin sojin saman Amurka da hedikwatar rundunar tsaro ta tsakiya da ke Jordan da makamai masu linzami.

Rundunar Sojojin Ruwa ta Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ta bayyana cewa harin ya kasance martani ne ga ayyukan ta’addanci na sojojin Amurka, wanda ta bayyana a matsayin “mai kisan yara.” Ta kara da cewa muddin barazanar da ake yi wa Iran ta ci gaba da dorewa kuma muddin aka ci gaba da aiwatar da ayyukan ta’addanci na sojojin Amurka kan muradun Iran, to za a ci gaba da yin turjiya.

Ta jaddada cewa dole ne a daina barazanar da tsoma baki ba bisa ka’ida ba na jami’an Amurka kan muradun Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted