Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci ya bayyana cewa;abokan gaba sun yi kuskuren lissafi akan Iran domin ba su tsammaci gwagwarmayar da suka fuskanta daga Iran ba.
Sayyid Abbas Arakci wanda aka yi hira da shi ta tashar talabijin ta cikin gida ya yi bayani akan yadda aka kafa kwamitin da zai rika kula da batun tattaunawa akan Shirin Nukiliyar Iran a karkashin Majalisar Koli ta tsaron kasa wacce ake kira da kwamitin bangarori shida.”
Dr. Abbas Arakci ya ce a tashin farko wannan kwamitin yana a karkashin shugabancin Shahid Shamkhani ne, daga bayan kuma ya koma karkashin shugabancin shahid Larijani, da ya zama babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasa.
Ministan harkokin wajen na Iran ya ce a karkashin wancan kwamitin an tattauna dukkanin batutuwan da su ka shafi Shirin Iran din na makamashin Nukiliya,wacce matsayarta ta karshe shi ne kin amincewa da daina tace sanadarin Uranium a cikin Iran.
Arakci ya kore cewa amincewa da rashin tace uranium ba zai hana afkuwar yaki ba, amma abinda zai faru idan an amince da hakan shi ne sayar da mutuncin kasa wanda ya fi yaki muni.
Bugu da kari, minstan harkokin wajen na Iran ya yi Ishara da yadda Netanyahy a ja Trump cikin yaki da zummar rusa jamhuriyar musulunci ta Iran. Sai dai kuma ba a je ko’ina ba abokan gaba su ka mika wuya ba tare da sharadi ba su ka kuma rattaba hannu da Iran akan fahimtar juna.
Ministan harkokin wajen na Iran ya ce Iran a matsayin babbar kasa ta tilsatawa Amurka zama kan teburin tattaunawa da kuma girmama jamhuriyar musulunci ta Iran.
Dr. Arakci ya ce;mun ki amince da bukatar da su ka bijiro da ita, ta tsayar da tace uranium wacce ba ta kan doka, da su ka ga cewa ba za su iya cimmata ba, sai su ka bude yaki.