Kakakin Majalisar Dokokin Iran Ya Yi Ba’a Ga Tunanin Amurkawa

Babban mai shiga tsakani na Iran kuma kakakin Majalisar Dokokin kasar Muhammad Baqi’r Qalibaf ya yi ba’a ga bayanan sirrin jami’an Amurka, yana mai da’awar cewa Amurkawa na ci gaba da kawo sabbin kayan aikin soja zuwa yankin Gabas ta Tsakiya yayin da suke ikirarin cewa suna son dakatar da yakin.

Rundunar Sojin Saman Iran Sun Kai Hari Kan Rumbun Makaman Amurka

Rundunar sojin Iran ta sanar da cewa, a wani sabon hari na jiragen sama marasa matuka ciki da kuma wani bangare na mataki na 17 na Operation Thunderbolt, ta kai hari kan wani rumbun makamai da kayan aiki mallakin rundunar sojojin Amurka ‘yar ta’adda a Kuwait.

Rundunar IRGC Ta Aike Da Sako Ga Al’ummar Kasar Kuwait

Sanarwar IRGC ta ci gaba da cewa: “Ya ku mutanen Kuwait masu daraja, sojojin Amurka marasa imani sun mamaye sassan Ć™asarku ta Musulunci tsawon shekaru, suna amfani da su a matsayin sansani don kashe Musulmai a Iran, Iraki, Afghanistan, da Falasdinu.

Shahadan Falasdinawa 13 Cikin Sa’o’i 24 Da Suka Gabata A Gaza

Rahotonni sun ruwaito cewa: Harin sama da sojojin Isra’ila suka kai kan unguwar Sabra ya nufi wani gini mai hawa uku a yankin da ke cike da jama’a ba tare da wani gargadi ba, inda ya yi sanadiyyar shahadan Falasdinawa biyar wadanda aka gano gawarwakinsu jim kadan bayan harin.