Yemen: Sojojin hayar Saudiyya 2,000 ne aka kashe da raunatawa

Kakakin rundunar da Saudiyya ke marawa baya a Yemen, karkashin jagorancin Tariq Saleh, ya sanar da cewa an kashe ko kuma jikkata sama da mayakansu

Sojojin yemen

Kakakin rundunar da Saudiyya ke marawa baya a Yemen, karkashin jagorancin Tariq Saleh, ya sanar da cewa an kashe ko kuma  jikkata sama da mayakansu 2,000 a yakin da ya barke a gabar tekun yamma.

Yana mai cewa har yanzu ana ci gaba da tatatra alkalumman asarorin da suka yi.

Kakakin ya bayyana cewa sojojin suna rasa daruruwan mayaka a kowace rana, wadanda aka kashe da kuma wadanda suka jikkata, yana mai bayyana wadannan alkaluma a matsayin wadanda aka saba gani kawai a manyan fadace-fadace da yaƙe-yaƙe.

Kakakin ya kuma bayyana cewa an kai wa sojojin hayar hari mai tsanani a lokacin da suke janyewa, tare da harba makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuki.

A wannan bagere ya nuna cewa jiragen sama marasa matuki 18 sun kai hari kai tsaye kan Tariq Saleh a hedikwatarsa ​​da gidansa, baya ga wasu cibiyoyin umarni da dama da ake kai hari kan su.

Sojojin Yemen na fafatawa da sojojin haya da Saudiyya ke marawa baya a larduna da dama, bayan hare-haren ba zata da aka kai kansu.

A halin yanzu, Saudiyya na kai hare-haren sama kan larduna da dama, ciki har da Marib, Al-Jawf, Taiz, da Hodeidah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted