Kakakin kwamitin tsaro da harkokin kasashen waje a majalisar dokokin kasar Iran ya bayyana cewa matukar gwamnatin kasar Amurka bata cika sharuddan JMI guda 7 ba, babu batun bude mashigar ruwa ta Hurmuz. Yace babu wani sauyi a matsayin kasar Iran.
Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya nakalto Hassan Qashqavi yana fadar haka a yau Lahadi a majalisar dokokin kasar ya kuma kara da cewa, dole ne aka cika wadannan sharuddan kafin a bude ta.
Qashqavi ya kara da cewa babbancin takardan fahintar juna ta Islamabad da kuma wanda Iran ta mikawa Amurka a birnin Newyork ta hanyar Qatar shi ne lokacin aiwatar da bukatun guda 7. Don haka har yanzun bukatun Iran na Islamabad ne ta sake mikawa kasar Amurka a NewYork amma ta takaita lokacin aiwatar da su. Haka kuma Iran ta sauya jerin yadda Amurka zata aiwatar da sharuddan.
Don haka a halin yanzu kwallo na hannun Amurka, zata mutunta alkawalin da shugabanta ya sanyawa hannu ko kuma a’a.