Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Janar Muhsen Rizaei ya ja kunnen Amurka da kawayenta kan cewa duk kuskuren lissafin da zasu yi nan gaba, zai su yi nadama don zasu gamu da manya manyan al-amuran da basu yi tsammani ba.
Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya nakalto Rezaie yana fadar haka a yau, ya kuma kara da cewa, shugaban kasar Amurka Donal Trump har yanzun yana mafarki, duk tare da abinda idonsa ya gane masa na hakikanin kasar Iran.
Rezaei ya kara da cewa, tare da shiryatarwar jagora mai hikima, da hadin kan mutanen kasa, da kuma hadin kan dukkan bangarorin gwamnatin JMI, Iran zata tsallaka wannan matsaloli masu sarkakiya da take fuskanta.
Daga karshe Rizaei ya bayyana cewa shugaban kasar Amurka dan ta’adda kuma makashin yara, zai gane hakikanin JMI nan gaba.