Sojojin Yemen Sun Kai Harin Ramuwar Gayya Kan Saudiyya

Rundunar Sojin Yemen ta fitar da sanarwar hare-haren da ta kai kan kasar Saudiyya a matsayin ramakon gayya Rundunar Sojin Yemen ta sanar da cewa

Rundunar Sojin Yemen ta fitar da sanarwar hare-haren da ta kai kan kasar Saudiyya a matsayin ramakon gayya

Rundunar Sojin Yemen ta sanar da cewa ta kai hare-hare biyu na soji ta hanyar amfani da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka ciki kan cibiyoyin man fetur na Aramco da ke biranen Riyadh da Khurais, a matsayin mayar da martani ga abin da ta bayyana a matsayin wani harin wuce gona da iri da Saudiyya ta kai wanda ya kunshi hare-haren sama da jiragen sama 50 da kuma hare-haren makamai masu linzami a cikin awanni 12 da suka gabata.

Kamfanin dillancin labaran Mehr ya ruwaito cewa: Rundunar Sojin Yemen ta sanar da cewa ta kai hare-hare biyu ta hanyar amfani da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka ciki kan cibiyoyin man fetur na Aramco da ke Riyadh da Khurais, a matsayin mayar da martani ga hare-haren jiragen saman Saudiyya kan kasar Yemen. Sanarwar ta ce: “Allah Madaukakin Sarki ya ce: {Duk wanda ya yi maka laifi, to ka mayar masa da martani kamar yadda ya yi maka laifi}. Hakika  Allah Madaukakin Sarki ya faɗi gaskiya.

Makiyin Saudiyya na aikata laifi ya ci gaba da kai wa mutanen Yemen hari ba bisa ka’ida ba, ta hanyar kai hare-hare masu tsanani, wanda a cikin awanni 12 da suka gabata ya kai hare-hare sau 50 na jiragen sama da makamai masu linzami kan babban birnin kasar Yemen Sana’a da kuma gundumomin Al-Jawf, Taiz, Amran, Hajjah da Sa’dah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted