Washington ta tabbatar da cewa ta janye jirgen yakinta samfurin B-1 daga sansaninin sojojin RAF Fairford na kasar Burtania zuwa gida.
Shafin yanar gizo na labarai Arabnew na kasar Saudia ya bayyana cewa, a yau Lahadio ce wani Jami’in Pentagon ya fadawa kafafen yada labaran Amurka daga ciki har da tashar talabijan ta CNN kan cewa Amurka ta dauke dukkan irin wadannan jiragen yaki daga Burtania zuwa gida saboda matsalolin tsaro.
A ranar 27 ga watan Satumban da ya gabata ne, wani manumi ya kira yansanda ya fadawa masu cewa yana tababan samuwar wasu motocin bus bus kusa da sansanin sojojin na RAF fairFord, amma a lokacinda yansandan fada da ayyukan ta’addanci suka garzaya zuwa can basu sami bom ko wani abin da zai tada hankali ba. Kuma mutane guda 5 da suka kama sun sakesu bayan yan sa’o’ii.
Labarin ya kara da cewa, a lokacinda aka tambayi mai magana da yawun firay ministan kasar Burtania Andy Burnham’s a yau Litinin yace sansanin yana cikin tsaro.
Wannan yana zuwa ne bayan da sakataren kungiyar tsaro ta NATO ya bayyana cewa, kasashen turai daga ciki har da kasar Burtania sun bawa Amurka dama kai hare hare kan Iran har sau 500 a yakin Ramadan da ya gabata.