Iran Ta Yi Tir Da Norway Kan Yada Internet Na Starlink Kan Kasar

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta gabatar da korafinta ga gwamnatin kasar Norway wacce take yada yanar gizo wato Internet na kamfanin starlink a cikin

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta gabatar da korafinta ga gwamnatin kasar Norway wacce take yada yanar gizo wato Internet na kamfanin starlink a cikin kasar Iran ba bisa ka’ida ba.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto

Darakta mai kula da zaman lafiya ta kasa da kasa a ma’aikatar hosain –Janad yana cewa kamfanin Starlink yana watsa yanar gizo a kasar Iran don amfanin Amurka da HKI da kuma ma’aikatansu a cikin kasar Iran ba bisa amincewa ba.

Daraktan ya kira jakadan kasar Norway a nan birnin Tehran Paul Bjornstad a jiya Lahadi, inda ya isar da wannan korafin kai tsaye ga gwamnatin kasar ta Norway, saboda rashin daukar mataki kan wannan al-amarin bayan korafi na farko.

Hossein-Nejad ya fadawa Jakadan Norway kan cewa Amurka da HKI suna ci gaba da amfani da yanar gizo na Starlink don taimakawa makiya da yan adawa da JMI don kifar da gwamnatin kasar.

Ya ce kasar Norway ce take rijistan kamfanin yanar gizo da Starlink a hukumar ‘ International Telecommunication Union (ITU), amma bata dauki wani mataki ba. Ya ce bisa bukatar JMI hukumar ITU ta bukaci Norway ta dakaatr da yada Starlink a kan kasar Iran amma har yanzun bata daina ba.

Banda haka Hosain Nejad ya mikawa jakadan na Norway wasika a rubuce ga gwamnatin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted