Rundunar IRGC: Iran Ba Ta Tsoron Barazanar Amurka

Shugaban masu ba da shawara ga babban kwamandan rundunar kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Mutanen Iran ba sa tsoron Amurka Shugaban masu

Shugaban masu ba da shawara ga babban kwamandan rundunar kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Mutanen Iran ba sa tsoron Amurka

Shugaban masu ba da shawara ga babban kwamandan rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta (IRGC) ya bayyana cewa: A karon farko, babu jiragen ruwan Amurka – ba kawai a Tekun Farisa, Mashigar Hormuz da Tekun Oman ba, har ma a arewacin Tekun Indiya.

A cewar kamfanin dillancin labaran Mehr, Birgediya Janar Ali Fadavi, shugaban masu ba da shawara ga babban kwamandan IRGC, ya ce: A cikin jawabin da aka watsa ta gidan talabijin: “Mashigar Hormuz, tsawon waɗannan watanni masu tsawo, hakika tana ƙarƙashin ikon Iran.”

Ya nuna cewa ƙarfin sojojin Amurka ya dogara ne akan teku, yana cewa: “Wannan yana nufin cewa sojojin ruwan Amurka sun haɗa da sojojin ƙasa da na sama. Saboda haka, tsarin ikon sojojin Amurka yana cikin sojojin ruwanta. Amurkawa suna nan a Tekun Farisa tun daga shekara ta 1853, amma yanzu, a karon farko, babu jiragen ruwan Amurka ba wai kawai a Tekun Farisa, Mashigar Hormuz da Tekun Oman ba, har ma a arewacin Tekun Indiya.”

Fadavi ya ƙara da cewa: “Amurkawa sun gudu sun ƙaura daga iyakokin Iran da nisan kilomita sama da dubu. Wannan lamari ba bisa ga zaɓinsu ba ne, a’a sakamakon ƙarfin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ne da kuma rundunar sojojin ruwa ta rundunar kare juyin juya halin Musulunci.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted