Aragchi Ya Ja Kunnen Yan Kasashen Wajen Da Suke Yankin Caucasus

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ja kunnen wasu kasashen waje wadanda suke shishigi a yankin Caucasus wanda zai iya hana zaman lafiya

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ja kunnen wasu kasashen waje wadanda suke shishigi a yankin Caucasus wanda zai iya hana zaman lafiya a yankin.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar iran ya nakalto Aragchi yana fadar haka, a yau litinin, ya kuma kara da cewa, a kyale kasashen yankin su samarda   tsaronsu a tsakaninsu.

Ministan ya fadawa tokwaransa na kasar Armenia Ararat Mirzoyan kan cewa, ya ji dadi da ganin an sami zaman lafiya tsakanin Azrbaijan da Armenia yana kuma fatan hakan zai dore.

A bangaren dangantaka tsakanin kasashen biyu kuma, ministan ya ce kasashen biyu zasu kara zurfafa dangantakar da ke tsakaninsu,  na tattalin arziki yawon shakatawa da al-adu da sauransu.

Mirzoyan, a na shi bangaren ya bayyana jin dadinsa da dangantakar da ke tsakanin Iran da Armenia ya kuma bayyana cewa, Yerevan zata ci gaba da kara kyutata dangantaka da JMI. Sannan Armenia zata fadada dangantaka da Iran a bangarorin tattalin arziki, siyasa, kasuwanci, sifiri da kuma makamashi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted