Yemen: Da Mashigar Ruwa Ta Babul Al-mandab Tana Hannummu

Kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen wacce kuma take iko da mafi yawan kasar ta sami nasarar kwace iko da tsibirin Mayyun dake dab da mashigar

Kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen wacce kuma take iko da mafi yawan kasar ta sami nasarar kwace iko da tsibirin Mayyun dake dab da mashigar ruwa ta babul –Mandab, wanda ya bata cikekken ikon kula da mashigar ruwan, wacce ta hada tekun Red  sea da kuma na tekun Aden,.

Kamfanin dillancin labaran Tesnim na kasar Iran ya bayyana cewa kafafen yada labaran kasashen yamma sun tabbatar da wannan labarin, kamar yanda France Press da BBC suka tabbatar.

Labarin ya kara da cewa kwace tsibirin Mayyun ya bawa gwamnatin San’aa ikon kula da duka jiragen da suke shigowa su fito daga babul Mandab, wanda tun watan yulin da ya gabata ta hana dukkan jiragen ruwa dauke da man kasar Saudia wucewa damatsigar.

Kafin nan ta hana dukkan jiragen ruwa mallakin HKI ko wanda yake da alaka da ita wucewa da yankin.

France Press ta nakalto Jami’an gwamnatin san’aa suna tabbatar da hakan, suna kuma yin kira ga yan kudancin kasar wadanda suke aikiwa kasar Saudia su ajiye makamansu wanda zai basu damar samun afuwar gwamnatin.   Kafin haka dai tsibirin na Mayyun yana karkashin ikon magoya bayan kasar Saudia.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted