Iran Ta Bada Sanarwan Taron Kasashen Na Bakin Tekun Farisa A Kasar Omman Nan gaba

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’ila Baghaei ya bada sanarwan cewa kasashen da suke bakin tekun farisa wadanda suka hada da Iran da Iraqi

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’ila Baghaei ya bada sanarwan cewa kasashen da suke bakin tekun farisa wadanda suka hada da Iran da Iraqi da kuma sauran kasashen yankin zasu gudanar da taro a birnin Mascat na kasar Omman a ranar litinin mai zuwa.

Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto Bakhaei yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kumakara da cewa, taron zai tattauna batun tsaron a yankin ne, ba tare da shigowar wata kasa wajen wadannan kasashe masu makobtaka da  tekun farisa ba.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya kara da cewa, za’a tattauna batun yarjeniyar da Iran da Omman suka cimma dangane da mashigar ruwa ta Hurmuz da kuma yanda shirin zaishafi kasashen yankin.

Daga karshe ya bayyana cewa, matukar sojojin Amurka sun ci gaba da kasnacewa a cikin tekun Omman ko nan kusa baza iya aiwatar da wani shiri ba, don haka dole ne wadannan kasashen su amince da rabuwa da neman tsaro daga kasashe wajen yankin tun farko.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted