Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, batun samar da kudade bai daya na kasashen kungiyar BRICS yana cikin al-amuran da kungiyar take tattaunawa a kansu a halin yanzu.
Kamfanin dillancin labaran ISNa na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana fadar haka a jiya jumma’a a gefen taron da shugaban kasar Iran Dr Masoud Pezeshkiyan yake yi da wakilan addinai daban daban a kasar Indiya, inda ake taron na shuwagabannin BRICS.
Aragchi ya kara da cewa, a halin yanzu dai dukkan kasashen kungiyar sun amince a karfafa musayar kudade da kasuwanci tsakanin kasashen kungiyar tare da amfani da kudaden cikin kasashensu, ba tare da dogaro da kudaden kasashen Amurka da na turai ba.
Yace, amma duk da haka batun samar da kudaden kasashen kungiyar tana nan kuma ana ci gaba da tattaunawa a kansu.