Wata sabuwar doka ta hana yan mata yan makaranta musulmi sanya hijabi a wuraren Jama’a daga ciki har da makarantun gwamnati da na masu zaman kansu ya fara aiki a kasar Autralia.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan kula da zamantakewa Claudia Bauer tana daga jam’iyyar Conservative OVP tana cewa tilastawa yan mata sanya hijabi wani kokari ne na hana su yenci da walwala kuma zaluntarsu ne. Don haka ne ma’aikatarta ta haramta hijabi da kuma sanya burka gay an mata yan kasa da shekaru 14.
Sai dai masu sukar dokan sun bayyana cewa, tana bayyana bambanci a fili ga wani bangare na masu bin wani addini a kasar Australia, wato musulmi ana son hanasu aikata addininsu.
Sannan Carla Amina Baghajati, wata Jami’a a kungiyar musulmi ta kasar Astralia (IGGO) ta shaidawa BBC kan cewa kungiyarta tana adawa da wannan dokar ta kuma kara da cewa “dokar rashin adalci ne wacce ta takaida hakkin musulmi na tafiyar da rayuwarta bisa tsarin addinin da tayi amani da shi. Kuma ya sabawa yenci.
Ta ce maimakon kare musulmi, sai suka zalunce shi ta hanyar takaita masa addininsa.