Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Iran ba zata taba durƙusawa Amurika ba, saboda Amurka ba ta son kasar ta ci gaba da zama ‘yantacciyar ƙasa
Shugaban kasar Iran Mas’oud Pezeshkian ya ce: “Idan Iran ta kalubalanci Amurka, to lallai zata kalubalanci gwamnatin yahudawan sahayoniyya, saboda mummunar dabi’arsu ta cin zarafin al’umma. Don haka Iran ba za taba durƙusa wa cin zarafi ba.”
Da yake jawabi a yammacin Juma’a a wani taro da shugabannin addinai, manyan mutane da ‘yan kasuwa a birnin New Delhi na Indiya, shugaban Iran ya ce: “Suna da’awar kare haƙƙin ɗan adam, amma waɗannan shaidanu ne waɗanda ke zargin al’umma nagari da zama ‘yan ta’adda. Shin mutanen kirki ‘yan ta’adda ne, ko su ne suka kashe yara 168 marasa laifi a cikin lokaci guda? Shin al’ummar Iran ne ‘yan ta’adda, ko kuma masu jefa bama-bamai da lalata jami’o’i, masu kashe masana kimiyya da mutane fararen hula? Idan suna jin su mayaka ne a kan tubalin zalunci, to al’umma ta gari zata tsage dantse ta yaƙe su, don gwada lallai za a iya kalubalanta azzalumai.”
Shugaban Iran ya nuna ire-iren matsin lamba da cin zarafin da Amurka ke yi wa al’ummar Iran, yana mai cewa: “Suna son dole sai an mika kai gare su, domin mutane su mika wuya saboda rashin albarkatu da sadarwa.” Amma al’ummar Iran ba za su yi kasa a gwiwa ba, kuma wannan ya samo asali ne daga imaninsu na dan Adamtaka da na addini.