Baqaei: Babu Ba’irane A cikin Yan 11 Ga Watan Satumba

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baqaei ya bayyana cewa wadanda suka aiwatar da hareharen 11 ga watan satumban shekara ta 2001 ba Iraniyawa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baqaei ya bayyana cewa wadanda suka aiwatar da hareharen 11 ga watan satumban shekara ta 2001 ba Iraniyawa bane, amma abinda ya tabbata a wannan al-amari Amurkawa kansu ne suka shirya hare haren don bawa kansu hujjar farwa kasashen musulmi su kuma mamayesu, abinda kuma ya faru bayan 11 ga watan satumba na shekara ta 2001 ne.

Baqaei ya bayyana haka ne a shafinsa na X a jiya Jumma’a 11 ga watan satumba ranar tunawa da wannan harin, da kuma maida martani ga sakataren harkokin wajen kasar Amurka wanda yake son danganta JMI da hare haren saboda ya halattawa kansa ci gaba da yakan kasar Iran.

Yace abinda ya faru bayan 11 ga watan satumba na shekara ta 2001 da kuma 2003, na mamayar kasashen Afganistan da Iraki ya nuna masa su waye hakikanin yan ta’adda.  Amurka da kawayenta sun kashe dubbai ko miliyoyin mutane maza da mata da yara da sunan yaki da ayyukan ta’addanci. Al-Hali su ne yan ta’addan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted