Bayan boren da bai yi nasara ba, an naɗa sabon shugaban rundunar soji a Nijar
Shugaban gwamnatin mulkin soja mai mulki a Nijar, Janar Abdourahmane Tiane, ya nada Birgediya Janar Mamman Sani Kiaou a matsayin sabon babban hafsan hafsoshin sojojin kasar a ranar Juma’a, inda ya maye gurbin Janar Moussa Salaw Barmo, a cewar gidan talabijin na gwamnati.
Duk da cewa sanarwar da aka watsa ta gidan talabijin ba ta bayyana dalilin korar Barmo ba, nadin ya zo ne bayan wani yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba a watan da ya gabata wanda ya girgiza ikon Tiane.
Magoya bayan gwamnati, tare da taimakon ƙungiyar African Legion (wadda a da ake kira Wagner Group), sun dakile wani yunƙurin tawaye bayan wani mummunan faɗa a babban birnin Niamey, inda sojoji suka kai hari kan wasu muhimman wurare kuma suka yi wa kansu katanga a cikin wani babban sansanin soja a filin jirgin sama.
Telebijin na gwamnati ya zargin Faransa da hannu a wannan bore, wanda ya faru a watan da ya gabata.