Baqa’i: Amurka Ba Ta Cancanci Ayyana ‘Yan Ta’adda Ba

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Amurka, a matsayinta na babbar mai tallafawa ta’addanci, ba ta cancanci hakkin tantance ‘yan ta’adda da ta’addanci

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Amurka, a matsayinta na babbar mai tallafawa ta’addanci, ba ta cancanci hakkin tantance ‘yan ta’adda da ta’addanci ba

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Isma’il Baqa’i ya yi ikirarin cewa: Amurka, a matsayinta na babbar mai tallafawa ta’addanci a duniya, ba ta da wata cancantar kafa mizanin ayyana ‘yan ta’adda da ayyukan ta’addanci a duniya.

A cikin wani rubutu da ya yi a dandalin X, Baqa’i ya mayar da martani ga ikirarin Sakataren Tsaron Amurka game da ta’addanci da kuma zarge-zargen da ya yi wa Iran, yana mai cewa: “Labarin Sakataren Tsaron Amurka game da ta’addanci a ranar tunawa da hare-haren 11 ga watan Satumba ya saba wa juna. Mutum ba zai iya yin yaki ba, ya aikata kisan gilla, da kuma kai hare-hare kan fararen hula yayin da yake ikirarin cewa yana fada da kuma ayyana ta’addanci.”

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya kara da cewa: Wadanda suka kai harin 11 ga watan Satumba ba ‘yan Iran ba ne, a’a, mutane ne da Amurka ta shirya kuma ta dauki nauyinsu a shekarun da suka gabata. Ko bayan harin 11 ga Satumba, abin da Amurka ta yi a Afghanistan da Iraki a karkashin sunan “yaki da ake yi da ta’addanci” ya haifar da kisan gilla da ya lakume rayukan fararen hula marasa laifi da kuma barna mai yawa a kasashen biyu.

Baqa’i ya kammala da cewa: Dangane da waɗannan hujjoji, amfani da tunawa da ranar 11 ga Satumba don tabbatar da yaƙi mai tsanani da aka yi da Iran, wanda ya kasance tare da kisan gillar da aka yi wa jami’an gwamnati da kuma kai hari ga fararen hula, ciki har da mata da yara, ba komai ba ne illa wani mummunan yunƙuri na halalta cin zarafi ba bisa ƙa’ida ba ta amfani da harshen yaƙi da ta’addanci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted