‘Yansanda a kasar Iran sun bada labarin cewa suna amfani da jiragen leken asiri da wasu kayakin masu aiki da lantarki na zamani don tabbatar da lafiyar masu tattalin 40 zuwa wurare masu tsarki a kasar Iraki.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Brigadier General Ahmad Ali Goodarzi shugaban yansanda a nan kasar Iran ya bayyana cewa, yansandan kasar suna aiki tare da rana wajen kyautata ayyukan tsaro a dukkan kofofi shiga Iraki daga Iran guda 6 saboda tabbatar da tsaron masu zuwa 40 na Imam Hussain (a).
Ya ce: Yansa a kan iyakokin kasar suna sanya kula da musamman a kofofin shiga kasar Iraki, wadanda suke da cinkoson mutane. Tare da amfani da jiragen marasa matuka wadanda suke da kayakin aiki na musamman don kula da su. Kuma suna aiki tare da tokwarorinsu na kasar Iraki a dayan bangaren na kasar.
Kofofin dai sun hada da Khosravi, Mehran, Shalamcheh, Chazzabeh, Tamarchin da kuma Bashmaq.
Ranar 40 na shahadar Imam Hussain (a) jikan manzon All..(s) a bana dai zai fada kan ranar 14 ga watan Augustan da muke ciki.