Gaza: Fiye Da Mutane 65 Ne Su Ka Yi Shahada Da Jikkata A Cikin Sa’o’i 48

Gaza: Fiye Da Mutane 65 Ne Su Ka Yi Shahada Da Jikkata A Cikin Sa'o'i 48 Saboda Ci Gaban Hare-haren Sojojin Mamaya
shahidan Gaza

Ma’aikatar lafiya a Gaza ta sanar da cewa adadin Falasdinawan da su ka yi shahada a cikin sa’o’i 48 sun kai 10, sai kuma wasu 56 da su ka jikkata da tuni an kai su asibitoci.

Ma’aikatar lafiyar ta Falasdinu ta kuma sanar da cewa; Da akwai adadi mai yawa na shahidai da suke kwance a karkashin baraguzai ba kuma za a iya isa gare su ba a wannan lokacin.

Haka nan kuma ma’aikatar kiwon lafiyar ta Gaza ta yi Ishara da cewa;tun daga ranar 11 ga watan Oktoba da aka sanar da tsagaita wuta, adadin shahidai sun kai 1.369,sai kuma wasu mutanen 4,627 da ‘yan sahayoniyar su ka jikkata. Haka nan kuma a wannan tsakanin an iya fito da gawawwakin shahidai 831 daga karkashin baraguzai.

Wata kididdigar kuwa tana nuni ne da cewa Daga farkon harin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kai wa Gaza a 7 ga watan Oktoba 2023, zuwa yanzu, adadin shahidai ya kai 73,783. Wadanda su ka jikkata daga wancan lokacin zuwa yanzu sun kai 147,738.

A wani labarin da tashar talabijin din almayadin ta dauka, ya ce wata mace mai ciki ta yi shahada tare jaririn dake cikin nata sanadiyyar raunin da ta samu kwanaki uku da su ka gabata daga Harbin sojojin mamaya a kudancin birnin Khan-Yunus.

Haramtacciyar Kasar ta yahudawa dai tana ci gaba da kai wa Gaza hare-hare ne duk da cewa an cimma yarjejeniyar tsagaita wutar yaki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted