An Yi Ganawa A Tsakanin Kwamandojin Sojan Iran Da Na IRGC

An yi ganawa a tsakanin kwamandojin soja da kuma na dakarun kare juyin musulunci na Iran inda bangarorin biyu su ka tattauna aiki tare domin
kwamandojin IRGC Da Soja Sun Gana

An yi ganawa a tsakanin kwamandojin soja da kuma na dakarun kare juyin musulunci na Iran inda bangarorin biyu su ka tattauna aiki tare domin dakile hare-haren Amurka da Haramtacciyar Kasar Isra’ila.

A yayin ganawar kwamandan dakarun kare juyi Janar Wahidi da kuma babban hafsan sojoji, Janar Hatami sun tabbatar da cewa; karfin da runudunonin sojojin kasar suke da shi, ya wuce duk yadda abokan gaba suke tsammani.

Bugu da kari, janar Wahidi ya ce; A tsawon lokacin yaki, abokan gabar sun ga karfin sojojin Iran, kuma ba domin ba domin taimakon Amurka ba,to da sojojin ‘yan sahayoniya sun rushe cikin lokaci kankane.

Haka nan kuma ya ce; Shugaban kasar Amurka Donald trump ya koma amfani da karairayi da yaudara, sannan cin karon da su ka yi tsayin dakar al’ummar Iran masu Imani, ya jefa mazauna fadar “White Hosue” cikin yanke kauna da sanyin gwiwa.

Kwamandan dakarun na IRGC ya kuma ce; Jami’an leken asirin Amurka da ‘yan sahayoniya da kuma sojojinsu sun yaudari shugabanninsu akan girman kalubalen dake gabansu akan Iran da yadda za ta iya yin tsayin daka da turjiya.

Shi kuwa hafsan sojan Iran Janar Hatami ya bayyana cewa; Aiki tare a tsakanin sojoji da kuma IRGC su ne ginshiki da kuma mabudin tabbatar da tsaro.”

Haka nan kuma  ya ce;Wannan hadin kan a tsakanin sojojin da dakarun kare juyin da yadda suke tafiyar da aiki tare, shi ne garkuwa ta hakikai dake kare kasa da dakille makirce-makircen makiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted