Iran : ‘Yan majalisa sun bukaci Daukar Fansar Jinin Shahidai

A yau Talata ne dai ‘yan majalisar shawarar musulunci ta Iran su ka fitar da bayani da a ciki su ka bayyana wajabci daukar fansar

A yau Talata ne dai ‘yan majalisar shawarar musulunci ta Iran su ka fitar da bayani da a ciki su ka bayyana wajabci daukar fansar jinin shahidai akan wadanda su ka tafka laifukan kashe su, tare da kuma da yin kiran a tsara yadda za a yi hakan.

Haka nan kuma ‘yan majlisar shawarar musuluncin ta Iran sun yi kira ga jami’an kasar da su dauki matakai kaifin wuka, su karfafa tsaron kasar.

Bayanin ya kunshi cewa:

“Daga mimbarin majalisa, muna yin alkawali,bisa amsa kiran malaman addini da yan majalisar kwararru masu girma, na aiwatar da kisasi akan wadancan masu laifukan,kuma ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen tsara matakan da za a yi aiki a su.

Haka nan kuma muna a tare da ku, ya kuma wadanda suke sadaukar da kawukansu.

Fiye da rabin ‘yan majalisar shawarar musuluncin ta Iran ne su ka rattaba hannu akan wannan sanarwar tare da bayyana batun daukar fansa da cewa; Jan Layi ne.

Bayanin ‘yan majalisar shawarar musuluncin ta Iran ya kuma yi jinjina ga al’ummar Iran da su ka fito kwansu da kwarkwatarsu a karkashin neman daukar fnasar jagoran al’umma shahidi.

Haka nan kuma sun yi jinjina ga al’ummar kasar Iraki saboda yadda su ka karbi bakuncin jagora shahidi a yayin jana’izarsa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted