Iran ta mayar da martani kan ikirarin jakadan Amurka cewa: Amurka ce mai kai harin wuce gona da iri, ba wacce aka zalunta ba
Jakadan Iran kuma wakilinta na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’id Iravani, ya yi fatali tare da mayar da martani kan ikirarin da jakadan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya ya yi, yana mai bayyana maganganun Amurka a matsaayin kalamai marasa tushe, yana mai tabbatar da cewa: Amurka ce mai cin zarafin bil’adama, ba wanda aka zalunta ba.
A cikin wata wasika da ya aika wa Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya da Shugaban Kwamitin Tsaron Majalisar Amir Sa’id Iravani ya ce: “Wakilin Amurka a taron Kwamitin Tsaro kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya, wanda aka gudanar a ranar Talata, 14 ga Yuli, 2026, karkashin ajanda mai taken ‘Kula da Zaman Lafiya da Tsaro na Duniya’ ya sake karkata daga ajandar kuma ya yi amfani da dandamalin Kwamitin Tsaro don yada labaran karya da kuma daidaita jerin zarge-zargen da ba su da tushe da kuma siyasa a kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.”
Ya ƙara da cewa: “Wakilin Amurka ya yi irin wannan zargi mara tushe a taron Kwamitin Tsaro kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya kan kasar Yemen, yana nuna tsarin bayanai marasa tushe da kuma amfani da tsarin Kwamitin Tsaro don dalilai na siyasa.”