Kungiyar tarayyar turai EU ta nuna cikakken goyon bayanta ga kotun hukumta laifukan yaki ta ICC kuma ta yi watsi da kokarin da gwamnatin Donald Trump ke yi na ganin an rusa kotu mai hukumta laifukan yaki ta kasa da kasa.
Kakakin kungiyar tarayyar turai Anouar El nouni ya bayyana cewa matsayin da kotun take da shi yana nana daram babu wani canji , kuma ya jaddada matsayin kungiyar naci gaba da yaki kan duk wani makirci da ake kullawa
Yace mun tsaya kyam wajen ci gaba da nuna goyon baya ga kotun ICC kuma yayi ishara game da rawar da kotun ke takawa wajen gurfanar da wadanda suka aikata wasu manyan laifuka a duniya da suka hada da kisan kare dangi laifukan yaki da kuma cin zarafin bil adama, don haka ba zaa taba amincewa da duk wani mataki da zai kawo cikas ga kotun ba
Wannan yana zuwa ne kwana daya bayan da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya sanar mataken da suke dauka na ganin an raje karfin da kotun ke da shi , kuma ya zargeta da tsoma baki cikin harkokin sojan Amurka da ayyukan da take gudanarwa kuma tana barazana ga karfin ikon Amurka