Rahotanni sun bayyana cewa ministan makamashi na kasar Rasha Sergey Tsivilyov ya isa birnin Tehran kuma ya gana da jami’an gwamnati game da muhimman batutuwa da suka hada da batun yarjejeniyar yin aiki tare a bangaren makamashi tsakanin kasashen biyu.
Ministan man fetur na kasar iran Muhsen Paknejad ya sanar cewa an cimma yajejeniyar kan manyan abubuwa da suka shafi iskar gas tsakanin kasashen iran da rasha kuma tuni aka gudanar da shirye-shiryen domin ganin an kammala da wuri.
Kana ya jaddada cewa hadin guiwa din bai takaita da shiga da fitarwa ba kawai, ya kunshi abubuwa da suka shafi yin zango da siya da siyar da iskar gas
Ana sa bangaren ministan makamashi na kasar rasha ya nuna gamsuwarsa game da ci gaban da aka samu kuma ya sanar da yarjejeniyar da kasashen biyu suka kulla za ta taimaka wajen kawar da duk wasu matsaloli daka iya kawo cikas wajen yin aiki tare.
Bayan wannan yarjejeniyar ana sa ran ministan man fetur na kasar iran zai kai ziyara birnin mosko nan gaba domin ci gaba da bibiyar lammuran.