Iran Ta yi Watsi Da Ikirarin Trump Na Tattaunawar Sao’i 11 A Kasar Oman, Kuma Tace Babu Wata Tattaunawa Da Amurka

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar iran kuma mai bada shawara kan harkokin kasashen waje Kazeem Garibabadi yayi watsi da ikirarin shugaban Amurka Donald trump  na

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar iran kuma mai bada shawara kan harkokin kasashen waje Kazeem Garibabadi yayi watsi da ikirarin shugaban Amurka Donald trump  na cewa Tehran ta tattauna da Washington na tsawon saoi 11, ya ce babu wata tattaunawa da ta gudana a kasar Oman tsakanin jami’an iran da na Amurka .

Garibabadi yace tattaunawar da jami’an iran suka yi a ziyarar baya bayan nan da suka kai kasar Oman ta takaita ne da tattaunawa da jami’an kasar Oman wanda bai da alaka da wata tattaunawa da jami’an  Amurka,  don haka babu gaskiya a ikirarin tattaunawa ta saoi 11 da kasar amurka, kuma mun yi watsi da ikirarin

A ranar litinin ne shugaban Amurka Donald tump ya shaidawa tashar fox news cewa masu tattaunawa na kasar Amurka sun yi Imani cewa sun cimma yarjejenia mai tsawo ta zaman lafiya da jami’an iran bayan kwashe saoi 11 ana tattaunawa a ranar 12 ga watan yuli sai dai shugabannin kasar iran sun gabatar da wasu sabbin bukatu.

Haka zalika garib abadi ya ce yayi imanin cewa mataken da suke dauka yayi daidai da yarjejeniyar fahimtar juna ta Islamabad kuma ya soki Amurka da yin watsi da nauyin da ya rataya a wuyanta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted