Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta sanar da lalata kayan aikin soja da tankunan mai mallakin rundunar sojin ruwa ta biyar ta Amurka a Bahrain
Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) ta sanar da cewa ta lalata cibiyar kula da NSI, babban rumbun adana kayan aiki da kayayyaki, da kuma tankunan mai mallakin rundunar sojojin ruwa ta biyar ta Amurka a Bahrain.
Tashar Sepah News, ta ruwaito cewa: IRGC ta sanar cewa: Jiya da daddare, sojojin wuce gona iri kan al’ummu na gwamnatin Amurka sun aikata ayyukan fashin teku a Tekun Indiya bisa hujjar iko da mashigar Hormuz. Sun yi yunkurin rufe hanyoyin ruwa ga jiragen ruwa da kuma hana duniya man fetur da iskar gas na yankin. A safiyar yau, sun fuskanci mayar da martani ga munanan ayyukansu ta hanyar wani mummunan hari da rundunar sojojin ruwa ta IRGC ta gudanar kansu.”
Sanarwar ta kara da cewa: “Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci sun lalata cibiyar kula da NSI, babban rumbun adana kayan aiki da kayayyaki na rundunar sojojin ruwa ta biyar ta Amurka a Bahrain.”
Sanarwar ta ci gaba da cewa: Maƙiya su sani cewa bayan waɗannan “‘yan fashi” sun rufe hanyoyin fitar da mai da iskar gas zuwa duniya daga Tekun Indiya, suna barazana ga muradun abokan hamayyar tattalin arzikin Amurka, to ya kamata su yi tsammanin rufe wasu hanyoyin fitar da makamashi waɗanda ke biyan muradun Amurka da ƙawayenta.