Kasar Ghana Na Shirin Baiwa Yan Kasar Da Aka Haifa A Ketare Damar Yiwa Kasa Hidima

Gwamnatin Ghana ta sanar da shirinta na samar da shirin yi wa kasa hidima, ga ƴan kasar da aka haifa kuma suka yi karatu a

Gwamnatin Ghana ta sanar da shirinta na samar da shirin yi wa kasa hidima, ga ƴan kasar da aka haifa kuma suka yi karatu a kasashen waje, don basu damar sanin asalinsu da kuma bada gudunmuwa wajen gina kasar.

Kofi Okyere-Darko, shugaban da ke kula da ƴan kasar mazauna kasashen waje da ke karkashin ofishin shugaban kasar ne ya bayyana hakan, a wajen taron kungiyar daliban Ghana da ke karatu a kasashen waje na wannan shekarar.

Ya ce shirin zai maida hankali ne kan matasa ƴan asalin kasar Ghana da aka haifa a kasashen ketare, inda za su yi wa kasarsu hidima  na tsawon watanni, wanda hakan zai basu damar sanin al’adunsu da dai sauransu.

Okyere-Darko ya jaddada cewar gwamnati ba za ta tilasta wa kowa ne dalibi komawa gida da zarar ya kammala karatun sa ba, amma abinda suke son cimmawa a karkashin wannan tsarin shi ne sanya musu kishin kasa ta yadda duk inda suka tsinci kansu ba za su mance asalinsu ba.

Shugaban ya bayyana daliban Ghana da ke kasashen waje a matsayin daya daga cikin manyan kaddarorin da kasar ke tinƙaho da shi, yana mai cewa suna wakiltar ƴan kasuwa da masu bincike da injiniyoyi da kwararru kan kiwon lafiya da kuma masu tsara manufofin kasar na nan gaba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted