Dakarun Sojin Iran Sun Ci Gaba Da Kai Hare-haren Mayar Da Martani Da Jirage Marasa Matuki A Sansanin Sojin Amurka

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin kasar iran sun kaddamar da hare-hare guda 8 a muhimman wuraren soji  Amurka dake yankin, kuma sun hari wurin

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin kasar iran sun kaddamar da hare-hare guda 8 a muhimman wuraren soji  Amurka dake yankin, kuma sun hari wurin da sujojin Amurka suke a kasar Jodan a matsayin mayar da martani kan hare-haren da Amurka take kai wa a yankuna daban daban a kasar iran.

Ofishin dake kula da hulda da jama’a na dakarun sojin kasar iran ya sanar cewa bisa la’akari da ci gaba da hare-haren zalunci da kasar Amurka take kawowa a kasar iran, an kaddamar da hare-haren guda 8 da sanyi safiyar yau laraba da sabbin jiragen sama marasa matuki a sansanin Al-azraq dake kasar Jodan

Kamar yadda yazo a cikin bayanan  wannan shi ne karo na biyu da aka kai harin inda jirgin sama mara matuki na kasar iran ya kai hari kan matsugunan jragen yaki kirar F-18 da kuma manyan wuraren ajiyar kayan ayyukan sojojin Amurka

A ranar litinin kakakin sojin kasar Iran ya gargadi Amurka cewa babu wani harinta da zai tilasta bude mashigar Hurmuz bayan matakin da iran ta dauka na rufe mashigar baki daya, saboda hare-haren da Amurka take kai wa.

Yace dole ne shugaban Amurka ta koyi yadda za ta girmama dokokin kasa da kasa  da kuma hakkokin kasashe da mutunci alumma, kamar yadda muka ambata tun da fari ba zaa taba iya bude mashigar Hurmuz ta hanyar yaki ba, ko kuma wani matakin hare-haren da Amurka za ta kai

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted