IRGC Ta Kai Hari Kan Sansanonin Amurka A Yankin

Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta sanar da kai sabbin hare-haren ramuwar gayya kan sansanonin sojojin Amurka Dake Kasashen Kuwait, Bahrain,

Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta sanar da kai sabbin hare-haren ramuwar gayya kan sansanonin sojojin Amurka Dake Kasashen Kuwait, Bahrain, da Jordan, bayan sabbin hare-haren da Amurka ta kai a wasu yankunan Iran.

A cikin sanarwar, IRGC ta yi Allah wadai da Amurka kan kai hari kan “sansanonin bakin teku da wurare da dama a lardunan kudancin Iran da makamai masu linzami da bama-bamai a cikin daren jiya.

Hare haren na Amurka na zuwa ne bisa lura da cewa “babu wani jirgin ruwa da ya yi yunkurin bin shawarar Amurka” na wucewa saboda rufe mashigin Hormuz da Iran ta yi.

A cewar IRGC, karo na hudu na Operation Nasr 2 ya kai hari kan “KJL,” wanda ta bayyana a matsayin, “babbar cibiyar jigilar kayayyaki ta rundunar sojojin Amurka a Yammacin Asiya da ke Mina Abdullah, a Kuwait.”

Hare haren karo na biyar an kai su ne kan cibiyoyin Amurka a Bahrain kan “Cibiyar Gudanarwa ta NSI, wacce ta kunshi manyan rumbunan adana kayan aiki na rundunar sojin ruwa ta Amurka a Bahrain.”

Hari na shida ya shafi sansanin jiragen sama na al-Azraq da ke Jordan, wadda ta kunshi jiragen yakin Amurka F-15, F-16, da F-35, sannan ta “kawar da wasu jiragen saman yaki marasa matuki na MQ-9 da ke sansanin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted