Gwamman yan majalisar dokokin birtaniya sun yi kira ga gwamnati da ta kakabawa Binjemin Natanyaho fira ministan isra’ila takunkumi da sauran ministocinsa game da azabatar da falasdinawa fararen hula da gwamnatin isra’ila ke yi
A cikin wata wasika da aka aike wa sakataren harkokin wajen birtaniya Yvette Cooper wanda akalla yan majalisar 71 suka sanyawa hannu da suka fito daga jam’iyu daban daban ya nuna cewa cikakkun bayanai da aka gudanar game da Azabtar da falasdinawa da gwamnatin isra’ila ke yi ya hada har da hannun fira ministan Banjemen natanyaho a ciki
Haka zalika yan majalisar sun bayyana cewa takunkumin da aka sanyawa wani minister a haramtacciyar kasar isra’ila Itamar ben Gvir a shekarar da ta gabata da kuma Bazalel Smotrich ya samu karbuwa sosai kuma ya kawo canji kadan game da yadda gwamnatin isra’ila ke muamala da falasdinawa da take tsare da su
Mai bincike ta musamman ta majalisar dinkin duniya Francesca Albanese game da yanyin hakkin dan adam a yankin falasdinu ta fadi a cikin rahotonta ga hukumar kare hakkin bil adama ta majalisar dinkin duniya cewa yanayin tsarin gidan yari Isra’ila ya koma tamkar wajen gwaje-gwaje na zalunci da aka kirkiro da suka kunshi ayyukan yi wa falasdinawa fyade da kwalabe, sandunan karfe, da kuma wukake.