‘Yan Lebanon Biyu Sun Yi Shahada A Harin Isra’ila

Mutane biyu sun mutu sakamakon hare-haren jiragen saman Isra’ila da kuma karuwar hare-haren kan kudancin Lebanon Hukumomin Lebanon sun sanar da mutuwar samari biyu a

Mutane biyu sun mutu sakamakon hare-haren jiragen saman Isra’ila da kuma karuwar hare-haren kan kudancin Lebanon

Hukumomin Lebanon sun sanar da mutuwar samari biyu a wani harin jirgin sama sojin haramtacciyar kasar Isra’ila ya kai, wanda ya yi daidai da hare-haren sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila da suka kai kan garuruwa da dama a kudancin Lebanon. Wadannan hare-haren sun hada da luguden harsasai, rusa gidaje, da kuma kona gonakin noma.

A cewar kamfanin dillancin labarai na kasar Lebanon, matasan biyu sun mutu ne lokacin da wani hari da jiragen saman sojin Isra’ila ya kai kan babur dinsu a yankin Doha Kufur Rumman da ke kudancin Lebanon.

Hukumar ta bayar da rahoton cewa kungiyoyin ceto sun gano gawarwakin Hussein Shukrun da Ahmed Roumani, dukkansu ‘yan shekaru 17, a ranar Litinin. Sun fito ne daga garin Deir Zahrani kuma sun bace tun bayan harin ranar Lahadi.

Sojojin mamayar Isra’ila sun ci gaba da ayyukan soji a sassa daban-daban na kudancin Lebanon. Hare-haren sun hada da lalata kadarori. Sojojin Isra’ila da ke zaune a garin Khiyam sun gudanar da ayyukan rushe gidaje a unguwannin yamma kusa da makarantun Al-Mabarrat. Hayaki ya tashi daga wurin, kuma an ji karar fashewar abubuwa a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted